15 Yuli 2026 - 13:40
Source: ABNA24
IRGC: Ta Kai Munanan Hare-Hare Kan Muhimman Wuraren Amurka A Safiyar Yau

Dakarun Juyin Musulunci: Cibiyar Gudanarwa ta NSI, Cibiyar Sarrafa Kwamanda, Manyan ɗakunan ajiyar kayan aiki da kayan soji da tankokin man fetur na rundunar ruwa ta biyar ta Amurka a Bahrain an murkushe su.

Kamfanin Dillancin Labarai na Ahlul-Bayt (a.s) - ABNA – ya bayar da rahoton cewa: Ofishin Hulda da Jama'a na Dakarun Juyin Musulunci na Iran: Al'ummar Iran masu jarumtaka da kafa tarihi; A daren jiya, Sojojin Amurka makasa yara da karya alkawari, tare da girke jiragen ruwansu a cikin Tekun Indiya, da iƙirarin sarrafa mashigar Hurmuz, sun toshe hanyoyin ruwa a kan jiragen ruwa, kuma sun hana duniya samun man fetur da iskar gas na yankin. Mayakan rundunar ruwa ta dakarun juyin musulunci da sanyin safiyar yau, da wani aiki mai ƙarfi, sun mayar da martani ga waɗannan ayyuka.

A zagaye na biyar na aikin "Nasr 2," da Kalmar sirri mai albarka ta "Ya Ali bin Abi Talib (A.S)," an murkushe tare da lalata cibiyar gudanarwa ta NSI da cibiyar bayar da umarni kwamandanci, manyan ɗakunan ajiyar kayan aiki da kayan soji, da kuma tankokin man fetur na rundunar ruwa ta biyar ta Amurka a Bahrain.

A ci gaban wannan sanarwa ya zo: Makiya su sani cewa yanzu da 'yan fashinsu suka toshe hanyar fitar da man fetur da iskar gas daga Tekun Indiya - wanda ke samar da muradun tattalin arizikin kawayen Amurka- dole ne su jira a rufe sauran hanyoyin fitar da man fetur da iskar gas waɗanda ke samar da muradun Amurka da kawayenta. Fitar da man fetur da iskar gas na yankin ko dai ya zamo ga kowa ko kuma ya zamo kowa ya rasa.

………..

Alamomi

Ra'ayinka

You are replying to: .
captcha